in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Kasar Sin za ta kafa kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin
2018-09-03 18:05:54 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa ta kudurin aniyar kafa kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin, don kara koyi da juna a fannin al'adu a tsakanin bangarorin biyu. A shekaru uku masu zuwa da ma wasu lokuta a nan gaba, kasar Sin za ta kyautata shirin nazari da cudanya tsakanin Sin da Afirka, kana za a gudanar da ayyukan al'adu da na yawon shakatawa guda 50, don goyon bayan kasashen Afirka su shiga kawance, ciki har da gidan nuna wasannin fasaha na kasa da kasa na hanyar siliki, da dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi, da bukukuwan fasaha da dai sauransu. Baya ga haka, za a bullo da wani tsarin hadin kai tsakanin kafofin watsa labarun Sin da na Afirka, da ci gaba da inganta cibiyar al'adu ga juna, da nuna goyon baya ga hukumomin ba da ilmi da suka dace da kasashen Afirka wajen neman samun iznin kafa kwalejin Confucious, da kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka da dama, ta yadda za su kasance wuraren da tawagogin Sinawa za su rika zuwa yawon shakatawa. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China