in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Xi Jinping ya fidda manyan matakai guda 8 na hadin gwiwar Sin da Afirka
2018-09-03 18:01:27 cri
Bayan "manyan shirye-shirye guda 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fitar a shekarar 2015, yau Litinin, ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su yi hadin gwiwa yadda ya kamata, domin mai da hankali kan aiwatar da "manyan matakai guda 8" cikin shekaru 3 masu zuwa, watau a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin raya harkokin masana'antu, da sadarwa, da cinikayya, da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da karfafa kwarewar kasa da kasa wajen gudanar da ayyukansu, da inganta harkokin kiwon lafiya, da musayar al'adu da kuma ayyukan kare tsaro.

Haka kuma, kasar Sin tana fatan ba da taimako na dallar Amurka biliyan 60 ga kasashen Afirka ta hanyoyin taimakon gwamnati, da hukumomin sha'anin kudi, da kuma zuba jari da dai sauransu, domin aiwatar da shirin "manyan matakai guda 8" cikin yanayi mai kyau. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin za ta kawar da bashi maras kudin ruwa da za a kawo karshen wa'adin biyansa nan da karshen shekarar 2018, na kasashen Afirka mafiya fama da talauci, da kasashen Afirka wadanda take bin dimbin bashi mai yawa, da kasashen Afirka masu tasowa da ba su da mashigin teku, da kuma na kasashen tsibirai masu tasowa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China