in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC# Sin za ta kafa wasu ma'aikatu 10 na Luban a nahiyar Afirka
2018-09-03 18:00:03 cri
A yayin taron kolin dandalin FOCAC da aka bude yau Litinin a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin kafa wasu ma'aikatu 10 da ake kira Luban don horar da matasan kasashen Afirka sana'o'i. Ma'aikatun Luban wani shiri ne na samar da horon sana'o'in da kasar Sin ta kafa a kasashen ketare, kuma kawo yanzu Sin ta kafa irin wadannan ma'aikatu a kasashen Thailand da Pakistan. Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin na goyon bayan kafa cibiyar hadin gwiwar Sin da Afirka kan kirkire-kirkire a yunkurin karfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire a tsakanin matasa, kuma za ta aiwatar da shirin horar da wasu mutne 1000 na kasashen Afirka wadanda suka kware kan fannoni daban daban, tare kuma da samar da kudin tallafin karatu na gwamnati ga matasan Afirka dubu 50 da ma horar da matasan kasashen Afirka dubu 50, baya ga haka, za ta kuma gayyaci matasan kasashen Afirka dubu biyu zuwa kasar Sin a matsayin shiri na musaya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China