in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Xi Jinping ya ce Sin za ta nunawa Afirka goyon-baya don cimma burin samun isasshen abinci kafin shekara ta 2030
2018-09-03 17:51:21 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin na goyon-bayan kasashen Afirka a kokarinsu na cimma burin tabbatar da samun isashen abinci kafin shekara ta 2030, kuma za ta yi kokari tare da kasashen Afirka wajen tsarawa gami da aiwatar da tsarin inganta hadin-gwiwarsu ta fannin zamanintar da ayyukan gona, da aiwatar da wasu muhimman ayyuka guda 50 na tallafawa kasashen Afirka wajen raya ayyukan gona, da samar da tallafin abinci da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan daya ga kasashen Afirka da suke fama da bala'i, da aikewa da kwararrun masana ayyukan gona dari biyar zuwa kasashen Afirka, da horas da kwararru matasa masu jagorantar fasahohin ayyukan gona, gami da masu jagorantar mutane don samun arziki ta hanyar gudanar da ayyukan gona. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta yanke shawarar gudanar da bikin baje-koli na hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, haka kuma tana baiwa kamfanonin kasarta kwarin-gwiwar kara zuba jari a Afirka, da ginawa gami da kara kyautata wasu yankunan hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannonin tattalin arziki da cinikayya a Afirka. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China