in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#An kara shigar da wasu kasashe uku a dandalin FOCAC
2018-09-03 17:20:57 cri
Shugaban kasar Sin a yau Litinin ya yi maraba da tawagogin wakilan kasashen Gambia da Sao Tome and Principe da kuma Burkina Faso da su halarci taron kolin dandalin hadin kan Sin da kasashen Afirka FOCAC da aka bude a nan birnin Beijing. Kasancewarsu sabbin mambobin dandalin, kasashen uku sun maido da huldar jakadanci tare da kasar Sin a watan Maris na shekarar 2016 da watan Disamban shekarar 2016 da kuma watan Mayun wannan shekara. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasashen Afirka 53, ta kuma kulla huldar abokantaka da wasu kasashen Afirka 24, ciki har da huldar abokantaka ta manyan tsare-tsare da hadin gwiwa daga dukkan fannoni. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China