in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kalaman Garba Shehu mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai dangane da taron kolin FOCAC na Beijing 2018
2018-09-03 15:45:36 cri


Malam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, a zantawarmu da shi ya bayyana cewa taron FOCAC yana da matukar alfanu ta fuskar ci gaban kasashen Afrika da ita kanta kasar Sin, bisa la'akari da mu'amalar cinikayya da tattalin arziki tsakanin bangarorin musamman yadda kasar Sin take jan kasashen Afrika a jiki wajen samun ci gaba tare ta fuskoki da dama kamar samar da ababen more rayuwa, aikin gona, layin dogo da sauran ayyukan da suka shafi kyautata rayuwar al'umma. Ya ce akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kasar Sin da Najeriya musamman bisa irin yadda kasar Sin ke samarwa Najeriya bashin kudaden gina ababen more rayuwa masu karancin kudaden ruwa. Malam Garba ya ce a halin yanzu akwai kamfanoni masu yawa na kasar Sin dake gudanar da ayyukan gina ababen more rayuwa a fannoni daban daban a Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China