in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Najeriya: Hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya samu ci gaba cikin sauri
2018-09-03 13:19:48 cri

Jakadan kasar Sin dake wakilci a tarayyar Najeriya Zhou Pingjian ya bayyana yayin zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a halin yanzu, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ya shiga wani sabon matsayi wato ya samu ci gaba cikin sauri, har ma sassan biyu sun samu babban sakamako a fannoni daban daban yayin da suke gudanar da hadin gwiwa. Ana kuma sa ran cewa, kasashen biyu za su kara samun sabon ci gaba bisa shawarar ziri daya da hanya daya ta hanyar yin amfani da damar shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.

Jakadan ya kara da cewa, kasar Najeriya ba ta samu ci gaba yadda ya kamata ba a fannin aikin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, haka kuma aikin yana shafar farfadowar tattalin arzikin kasar matuka, a don haka sassan biyu wato Sin da Najeriya suna mai da hankali sosai kan hadin gwiwa a wannan fannin, musamman ma wajen gina layin dogo a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Kana matsayin cinikayyarsu shi ma ya bunkasa sannu a hankali, kasar Sin ta ci gaba da zama babbar kasa ta uku wadda ke gudanar da cinikayya da nahiyar Afirka.

Jakadan ya ci gaba da cewa, taron kolin dandalin FOCAC da ake gudanarwa a nan Beijing ya hada shawarar ziri daya da hanya daya, da ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD, da ajandar raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063 ta AU da kuma tsare-tsaren raya kasa na kasashen Afirka daban daban sosai, tabbas taron kolin zai biya bukatun ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, ana cike da imani cewa, taron kolin zai ciyar da huldar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya, da kuma huldar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka gaba kamar yadda ake fata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China