in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron ministocin FOCAC karo na 7 a birnin Beijing
2018-09-02 17:22:49 cri

A yau ne aka gudanar da taron kolin ministocin dandanlin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka(FOCAC) karo na 7 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Mamba a majalisar zartarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwaransa na cinikayya Zhong Shan ne suka jagoranci taron tare da ministar dangantaka da hadin gwiwar kasa da kasa ta Afirka ta kudu Lindiwe Sisulu da na cinikayya da masana'antu Rob Davies.

Minista Wang ya ce, mahalarta taron sun hada da ministocin harkokin waje ko wakilan harkokin tattalin arziki da cinikayya daga kasashen Afirka mambobin FOCAC da manyan wakilan hukumar zartarwar kungiyar AU 53. Taron na bana shi ne cikon shekaru 18 da kafa dandalin na FOCAC kana dandalin ya kasance abin koyi kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa da alakar kasa da kasa tsakanin kasashen Afirka.

Yayin taron kolin FOCAC na Beijing, ana saran shugaban kasar Sin Xi Jinping a madadin gwamnatin kasar Sin zai gabatar da matakan raya kyakkyawar makomar al'ummar Sin da Afirka ta bai daya a nan gaba da sanar da wasu matakan da kasar Sin ta dauka domin karfafa alakar Sin da Afirka a nan gaba. Taron kolin zai kasance na tarihi da zai kara karfafa alakar tsakanin Sin da Afirka.

A jawabinta uwargida Sisulu, ta ce kasashen Afirka sun yaba da goyon baya da taimakon da kasar Sin ta dade tana ba su, sun kuma yaba da irin tarin nasarorin da Sin ta samu, suna kuma fatan yi koyi da matakan da kasar ta Sin ta yi amfani da su wajen samun ci gaba.

Ta kara da cewa, kasashen Afirka za su hada kai tare da kasar Sin ta yadda za a samu nasarar taron kolin FOCAC na Beijing.

A yayin taron ne kuma aka yi maraba da kasashen Gambia da Sao Tome and Principe da Burkina Faso a matsayin sabbin mambobin FOCAC. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China