Mnangagwa ya ce, tsarin dandalin FOCAC ya samar da wani kyakkyawan zarafi ga kasashen Afirka wajen samun ci gaba, kana, a karkashin wannan tsari, gwamnatin kasar Sin ta samar da dimbin taimako da goyon-baya ga kasashen Afirka. Ya ce sabuwar gwamnatin Zimbabwe za ta yi amfani da damammakin da kasar Sin ta ba ta don neman samun ci gaba.
Wannan shi ne karon farko da Mnangagwa ya kawo ziyara kasar Sin tun bayan da ya lashe babban zaben kasar ta Zimbabwe, kana, karo na biyu da ya kawo ziyara kasar Sin a bana.(Murtala Zhang)