in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar Sin da Afirka na da muhimmanci ga zaman lafiya da ci gaban duniya, in ji Antonio Guterres
2018-08-31 20:04:02 cri
Jiya Alhamis, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana a hedkwatar MDD cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka tana da muhimmiyar ma'ana ga zaman lafiya da ci gaba na kasa da kasa.

Ana saran Guterres zai halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Yayin ganawa da 'yan jaridun kasar Sin a wani taron manema labaran da aka shirya a birnin New York, Mr. Guterres ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wani muhimmin mataki ne a kokarin da ake na taimakawa kasashen Afirka na neman ci gaba, wadda ta dace da ajandar MDD na samun dauwamamman ci gaba nan da shekarar 2030.

Taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da za a yi a birnin Beijing yana da muhimmanci matuka wajen karfafa shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Sin da Afirka kan batun hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka wani muhimmin bangare ne na shawarar "Ziri daya da hanya daya", ba kawai ya shafi hadin gwiwar tattalin arziki ba, har ma yana kyautata tsarin ci gaban tattalin arziki na duniya, lamarin da ya habaka dunkulewar kasa da kasa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China