in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin kamfanonin Sin da Afirka zai mai da hankali kan batutuwa 3
2018-08-31 19:21:05 cri
A yau Jumma'a, a yayin taron manema labaru na farko da aka gudanar a cibiyar watsa labaru ta taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2018 dake birnin Beijing na kasar Sin, an sanar da cewa a yayin taron musayar ra'ayi tsakanin shugabannin Sin da Afirka da wakilan shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu, kana taron shugabannin kamfanonin Sin da Afirka, an sanya batutuwa 3 da za a tattauna a kansu, wadanda suka hada da: na farko, sa kaimi ga hadin gwiwa a fannin raya masana'antu, da tabbatar da samun moriya da ci gaba tare; sai na biyu, zurfafa hadin gwiwa a fannin cinikayya; kana na uku, kara yin hadin gwiwa a fannin kayayyakin more rayuwa, da neman samun ci gaba mai dorewa. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China