in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Botswana da na Somaliya
2018-08-31 16:23:42 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, a yau Jumma'a a dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana son kara tuntubar juna tare da kasar Botswana a kan manufofinsu, kana tana maraba da kasar Botswana wajen halartar aikin "ziri daya da hanya daya". Ya ce ya kamata a kara sa kaimin hadin gwiwar kasashen biyu ta fannonin mu'amalar al'adu, da kiyaye namun daji tare.

A nasa bangare, shugaba Masisi ya bayyana cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak, kuma tana nuna godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da take nunawa ga kasashen Afirka wajen yaki da mulkin mallaka da neman 'yancin al'umma da ci gaban kasa. Kana ya amince da tunanin al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da nuna goyon baya ga shawarar "ziri daya da hanya daya", tare da yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu bisa tsarin FOCAC.

A wannan rana, shugaba Xi Jinping ya kuma gana da shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo, inda ya jaddada cewa, Sin tana murnar samun babban ci gaba, a yunkurin shimfida zaman lafiya da ake yi a kasar Somaliya. Kana za ta ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Somaliya, a fannin siyasa, da sulhuntawa a tsakanin al'umma, da kuma inganta kwarewar kasar wajen gudanar da harkokin kasar .

A nasa bangare, shugaba Mohamed ya bayyana cewa, kasar Somaliya tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen tabbatar da kyakkyawar makomar bai daya a tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China