in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka a idon Xi Jinping
2018-08-31 14:20:20 cri

Kasar Sin da kasashen Afirka suna da dadadden zumuncin tsakaninsu, a don haka suna goyon bayan juna, suna taimakawa juna a ko da yaushe, har ma suna ta karfafa hadin kai a fannoni daban daban. Yau ga wasu labarai da abokiyar aikinmu Bilkisu ta hada mana, kan hadin kai dake tsakanin sassan biyu a idon shugaban kasar Sin Xi Jinping.

A yankin dake gabashi maso tsakiyar babbar nahiyar Afirka, akwai wata hanyar dogo mai tsawon kilomita sama da 1800, wadda har yanzu ake amfani da ita, duk da cewa tana da tsawon tarihi na shekaru 40 da wani abu. A shekaru 70 na karnin da ya wuce, kasar Sin wadda ita ma ke fama da talauci, ta tallafawa kasashen Tanzania da Zambia wajen gina wannan hanyar dogon, har ma hanyar dogon ta kasance wata alama ta nuna zumunci a tsakanin Sin da Afirka.

A karkarar dake kudu maso yammacin birnin Dar es salaam dake bakin teku a gabashin kasar Tanzania, akwai wani filin kaburbura, inda aka binne Sinawa 69 da suka mutu, sakamakon ayyukan taimakawa kasar ta Tanzania wajen gina kasar, yawancinsu sun rasu ne sakamakon aikin gina hanyar dogo a tsakanin Tanzania da Zambia. A watan Maris na shekarar 2013, a yayin ziyararsa ta farko bayan ya kama kujerar shugaban kasar Sin, sai Xi Jinping ya yi makoki a wadannan kaburbura,

"A shekaru 40 da suka gabata, Sinawa sama da dubu 50 sun zo nan kasar, inda suka yi kokari tare da 'yan uwanmu na Tanzani da Zambia, sun kawar da wahalhalu da yawa, har ma sun kafa wannan hanyar dogo ta Tanzania da Zambia da ake kiranta 'hanyar sada zumunci' da 'hanyar 'yanci'. Mutane sama da 60 daga cikinsu sun rasa rayukansu sakamakon haka. Lallai su jarumai ne na sada zumunci a tsakanin Sin da Tanzania, da Sin da Afirka. Za a yi ta tunawa da sunayensu a zuciyar jama'ar kasashen Sin da Tanzania da Zambia har abada."

Ta hanyar tunawa da kwararrun kasar Sin da suka mutu sakamakon ayyukan tallafawa Tanzania ne, shugaba Xi ya gayawa duniya cewa, sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka ba bisa wani sharuda ba, yana dogaro da zumunta dake jure jarrabawar tarihi.

Yanzu bisa jagorar shawarar "Ziri daya da hanya daya", ana ta inganta hadin kai a tsakanin sassan biyu a manyan kayayyakin more rayuwa da dama. Tsawon hanyoyin dogo da Sin ta ba da taimakon ginawa a fadin nahiyar Afirka, ya wuce kilomita 6200, a yayin da tsawon hanyoyin mota ya wuce kilomita 5000.

Baya ga haka, kasar Sin da kasashen Afirka suna kuma karfafa hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya. A watan Disamba na shekarar 2015, shugaba Xi Jinping ya kai ziyararsa ta biyu a nahiyar Afirka, inda ya halarci babban taron masu masana'antu na Sin da Afirka, a cikin jawabinsa ya ce,

"Afirka a yau na cike da kuzari, hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta kai wani sabon matsayi da ba a taba gani ba a tarihi. Masu masana'antu da yawa na kasar Sin suna zuba jari, da gudanar da ciniki a kasashen Afirka. Abokanmu na Afirka ma suna zuwa kasar Sin don gudanar da ciniki. A lardin Zhejiang inda na taba aiki, akwai wani karamin birni mai suna Yiwu, wanda ake kiransa 'Birni na kananan kayayyakin cinikayya'. Yanzu haka akwai dubu duban 'yan kasuwan Afirka dake zaune a can, suna gudanar da cinikayya tsakanin Sin da Afirka."

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, da sahihiyar zuciya Sin ke fatan more fasahohin da ta samu tare da kasashen Afirka. Tana kuma fatan nunawa kasashen Afirka goyon baya a fannonin kudi, da fasaha da kuma kwararru don raya masana'antunsu. Sin na maraba da kasashen Afirka da su yi amfani da damar ci gabanta, don sanya nasarorin da ta samu za su amfana wa jama'ar kasar Sin da na Afirka mafi yawa.

A yayin ziyarar kuma, shugaba Xi Jinping ya sanar da manyan shirye-shirye 10, na hadin kai a tsakanin Sin da Afirka a shekaru 3 masu zuwa, don kara saurin raya masana'antu da zamanintar da aikin gona. Hakan a cewar sa zai taimakawa Afirka wajen samun dauwamammen ci gaba bisa karfin kanta.

A karkashin kokarin da sassan biyu ke yi, an samu hakikanan nasarori wajen hadin kansu a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Bisa kididdigar da aka yi, an ce a shekartar 2017, jimilar cinikayya a tsakanin su ta kai dalar Amurka biliyan 170. Da hakan kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ta farko ta Afirka a cikin shekaru 9 da suka wuce a jere. Ita ma nahiyar Afirka ta kasance babbar kasuwa ta 3 da Sin ke zuba jari a ketare, kuma babbar kasuwa ta 2 da Sin ke yin kwangilar gine-gine a ketare. Jimilar jarin da Sin ke zubawa nahiyar Afirka ta wuce dalar Amurka biliyan 100, wato ta ninka ta shekarar 2000 har sau dari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China