in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afrika za su karfafa hadin gwiwa da goyon bayan juna a taron kolin FOCAC na Beijing
2018-08-31 09:58:17 cri
Wani babban jami'in kungiyar tarayyar Afrika AU ya ce taron kolin (FOCAC) da za'a gudanar a Beijing na kasar Sin, zai kasance a matsayin wani dandali inda Sin da kasashen Afrika za su yi amfani da wannan dama wajen daukar matakan da za su tabbatar da kara gina dangantakar dake tsakaninsu da tallafawa harkokin cinikayya na gamayyar kasashen.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Alhamis a Addis Ababa, kwamishinan AU mai kula da harkokin ciniki da masana'antu Albert Muchanga, ya ce FOCAC wata dama ce da kasar Sin da kasashen Afrika za su yi amfani da ita wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a dukkan fannoni don cin moriyar juna.

An shiya gudanar da taron kolin FOCAC na Beijing ne a ranakun 3 zuwa 4 ga watan Satumba mai zuwa, wanda aka yiwa taken, "Sin da Afrika: karfafa dangantaka a nan gaba ta hanyar hadin gwiwar moriyar juna."

Ya jaddada cewa, bangarorin biyu suna yin hadin gwiwa game da batutuwa da dama daga ciki akwai batun tabbatar da zaman lafiya da tsaro, samar da kayayyakin more rayuwa da bunksa masana'antu, Muchanga ya ce taron kolin dake tafe zai kara daga matsayin hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China