in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zumuncin Kasar Sin Da Afirka Ya Karfafa
2018-08-31 09:20:50 cri
Kasar Sin ta fifita karfafa dankon zumunta da sauran kasashen duniya a matsayin wani mahimmin abu a huldarta da kasashen waje. A bisa zuwan da kungiyar yaukaka dangantaka a tsakanin Sin da Nahiyar Afrika (FOCAC) ta yi, akwai wajibcin bukatar Nijeriya ta shiga cikin shirin taro na 18 wanda za a yi a Beijing, wata mai zuwa a matsayin wani mataki na karfafa dangantakar kasashen biyu.

An kafa kungiyar ta FOCAC ne a shekarar 2000, a karkashin wani shirin karfafa dangantaka da taimakon juna a tsakanin kasar ta Sin da kuma kasashen Afrika. Taro na baya-bayan nan an yi shi ne a Johannesburg, na kasar Afrika ta kudu, a shekarar 2015. Wakilai daga kasashen Afrika 50 ne gami da ita kanta kungiyar ta kasashen Afrika suka halarci taron.

Sin ta samar wa nahiyar Afrika jimlan kudi dala bilyan 60 na bashi da kuma kudin fito. Daga cikin wannan kudaden dala bilyan 5 duk na gudummawa ne da kuma basukan da babu ruwa a cikin su. kasashe 53 ne na nahiyar ta Afrika da suka hada da Nijeriya wadanda suke da huldan jakadanci da kasar ta Sin ake sa ran za su halarci wannan taron na kwanan nan.

Shugaban kasar ta Sin, Xi Jinping, da yake tsokaci kan mahimmancin wannan taron, ya bayyana cewa, dangantaka a karkashin kungiyar ta FOCAC, ya doru ne a kan abubuwa biyar, daidaiton siyasa da aminci da juna, amfanuwa da juna da hadin kai na tattalin arziki, musayar al'adu, hadin gwiwa ta fuskacin tsaro da taimakon juna gami da hadin kai ta fuskacin al'amurran kasashen waje. Wadanda wadannan duk za su amfani Nijeriya ne. Gabakidayan Afrika tana da matsalar samar da manyan ayyuka, wanda a yanzun haka kasar ta Sin ta nuna a shirye take da ta taimaka kan hakan, wanda daya daga cikin su shi ne gina mana manyan titunan Jiragen kasa. Wanda ko don hakan akwai hikiman mu karfafa dangantakar mu da kasar da ta kasance ta biyu a bisa karfin tattalin arziki a duniyar nan wacce a shirye take da ta tarbe mu da hakan, kuma take shirye da ta hada kai da mu ta fuskacin kasuwanci.

Haka nan kuma, kungiyar ta FOCAC tana da dangantaka da mahimmin shirin nan na samar da tsarin hadin kai a duniya na gwamnatin ta Sin mai suna, "Belt and Road Initiative", wanda Shugaban kasar ta Sin, Xi Jinping, ya kaddamar da shi a shekarar 2013. Wanda aka gina shi a kan samar da sassaukar hanyar habaka kasuwanci da kuma musaya a tsakanin mutane.

Don haka, sai ya zama ba abin mamaki ne ba, cewa daya daga cikin manyan taken taron na kungiyar ta FOCAC, shi ne hada BRI da shirin Majalisar dinkin duniya na samar da ci gaban duniya ya zuwa shekarar 2030, shirin kungiyar Afrika ta AU da kuma samar da dubarun habaka tattalin arziki na kasashen na Afrika kamar dai farfado da tattalin arzikin Nijeriya da habaka shi. Tuni aka fara kaddamar da wannan shirin, ana kuma samun ci gaba a wannan dangantaka a tsakanin kasar ta Sin da kuma kasashen na Afrika mahimman fannonin da suka shafi masana'antu, noman zamani, manyan aikace-aikace, kawar da talauci, ayyukan lafiya, kasuwanci da zuba jari, al'amurran tsakanin mutane da mutane, musayar al'adu, zaman lafiya da tsaro.

Haka nan, yawan kasuwanci a tsakanin kasashen na Afrika da kasar ta Sin shi ma ya karu daga dalar Amurka biliyan 10.6, zuwa dalar ta Amurka biliyan 170 daga shekarar 2000 zuwa shekarar 2017. Shi ma jarin da kasar ta Sin ta zuba a fannonin kasuwancin na Afrika ya haura daga dalar ta Amurka miliyan 500 ya zuwa sama da dala biliyan 41 a daidai wannan lokacin da ake magana a sama. Wannan duk yana daga cikin mahimmancin kungiyar ta FOCAC ne a Nijeriya. Duk kasashen biyu, Nijeriya da Sin, suna aiki tukuru na ganin sun samar da dubarun ci gaba mai amfani a tsakanin su.

Ita ma Nijeriya ta karbi shirin nan na farfado da tattalin arziki da tsarin habaka shi, (ERGP) da kuma manufar ta na shekarar 2020. Titin jirgin kasa na tsakanin Abuja zuwa Kaduna da kuma jirgin kasa mai yawo a cikin gari na Abuja, duk sakamakon wannan shirin ne na tsakanin kasar ta Sin da Nijeriya da kuma kungiyar hadin kai a tsakanin Sin da nahiyar Afrika.

A yanzun haka, Sin ta himmantu wajen daukan matakai ta hanyar kulla yarjejeniya domin taimakawa a samar da manyan ayyukan raya kasa wadanda kasar nan take matsanancin bukatar su, da za su daukaka matsayin ta. Haka nan matsayin Nijeriya ba wai na kasa mai yawan al'umma a Afrika ba kadai, a matsayinta na kasa mafi girman tattalin arziki a Afrika, babbar kasuwa ce ga tattalin arzikin kasar ta Sin wanda ya rigaya ya daukaka. Ra'ayinmu ne, kasashen biyu duk suna da abubuwa masu kama da juna da za su iya karuwa da su ta fuskacin habaka tattalin arzikinsu, wanda ya kamata su kara kusantar juna da hadin kai a tsakanin su.

Ta kungiyar ta, FOCAC ne ya kamata su fara, fatan mu shi ne, giwayen kasashen biyu a yankunan su, za su yi amfani da wannan taron wajen kara kusantar juna domin su kara cin gajiyar hadin kai a tsakanin su. Tabbas kasashen biyu za su ci gajiyar amfanin musayar ra'ayi a tsakanin su.    (Umar A. Hunkuyi, Ma'aikacin Jaridar LEADERSHIP A Yau, daga Nijeriya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China