in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron FOCAC: A Yau Juma'a Tawagar Shugaba Buhari Ke Barin Nijeriya Zuwa Kasar Sin
2018-08-31 09:18:29 cri
A yau Juma'a ake sa ran Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tashi zuwa kasar Sin domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin Afirka da Kasar Sin.

Daga cikin tawagar da za ta rufa wa shugaban kasar baya akwai Ministoci guda tara da kuma Gwamnoni hudu da kuma wasu Sanatoci.

Sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasan na Musamman a kan yada labaru, Malam Garba Shehu ya fitar a jiya Alhamis, ta bayyana cewa Shugaban Kasa Buhari zai halarci taron ne da za a yi karo na bakwai wanda aka shirya fara gudanar da shi daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumban nan a Babban Birnin Kasar Sin, Beijing.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kafin taron, Shugaba Buhari zai fara ganawa da 'Yan Nijeriya mazauna Kasar Sin a ofishin jakadancin Nijeriyar da ke kasar.

Kafin bude taron Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, zai fara gabatar da jawabi, wanda zai bayar da damar tattaunawa tsakanin shugabanin kasar Sin da na kasashen Afirka da wakilan 'yan kasuwa da masu masana'antu a kasashen Afirka.

Ya ci gaba da cewa Shugaban Nijeriyar zai hadu da Shugaban kasar Sin Xi Jinping da wasu shugabannin kasashen Afirka domin fara taron na bana mai taken: "Hanyoyin karfafaf juna tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka."

Sanarwar ta cigaba da cewa, "Lokacin da aka yi taron karo na hudu a cikin watan Disamba na shekara ta 2015 shi ne lokaci na farko da shugaban ya halarci taron wanda aka yi shi a Johannesburg, Afirka ta Kudu, sannan wasu jihohi sun ziyarci kasar Sin a watan Afirilu na shekara ta 2016. Saboada haka, wannan Gwamnati ta ci gaba da kulla hulda tsakaninta da kasar Sin a kan samar da ababen more rayuwa da kasuwanci da harkokin zuba jari da samar da wutar lantarki da noma da ilimi da sauran su".

Haka kuma daga cikin wadanda za su raka shugaban kasar akwai Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na Bauchi, da Akinwunmi Ambode na Legas, da Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa da Rochas Anayo Okorocha Gwamnan jihar Imo.

Haka kuma akwai ministan kasashen waje, Geoffrey Onyeama; da ministan sufuri, Rotimi Amaechi; da ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola; da ministan birnin tarayya, Muhammad Bello; da ministan masana'antu da kasuwanci da zuba jari Okechukwu Enelamah; da ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma; da ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu; da karamin ministan albakatun man fetur, Ibe Kachikwu, da kuma karamin ministan filin jirgin sama, Hadi Sirika.

Sauran sun hada da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno; da babban daraktan kamfanin samar da man fetur na Nijeriya, Maikanti Baru.

(Abdulrazaq Yahuza Jere da Sabo Ahmad, Ma'aiakatan Jaridar LEADERSHIP A Yau, daga Nijeriya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China