in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bullo da dokoki da tsare-tsare don karfafa shawarar Ziri daya da Hanya daya
2018-08-30 19:48:01 cri
Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta furta a yau Alhamis cewa, yadda aka kafa kwamitin kwararru masu kula da cinikin kasa da kasa a kotun kolin kasar Sin, wani sabon matakin ne da na tabbatar da hadin gwiwa a fannin shari'a karkashin shawarar Ziri daya da Hanya daya, wanda zai taimaka wajen daidaita sabanin ra'ayi a fannin cinikin kasa da kasa cikin adalci.

Ban da haka kuma, game da yadda wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ke kokarin shafa wa kasar Sin cewar wai kasar Sin ta sanya tarko na bashi ga wasu kasashe, Madam Hua ta ce, rancen da kasar Sin ta baiwa wasu kasashe sam babu wani sharadin siyasa a cikinsa. Don haka ta bukaci masu yada jita-jita da su daina gurgunta kokarin da ake yi domin taimakawa wasu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China