Madam Ahunna na daya daga cikin jami'an tawagar MDD da za su zo birnin Beijing don halartar taron kolin dandalin FOCAC a farkon watan Satumba, karkashin jagorancin babban sakataren MDD Antonio Guterres.
Yayin da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanakin baya, Madam Ahunna ta ce, kasashen Afirka da kasar Sin na da kamanceceniya da yawa, abun da ya sa hadin-gwiwarsu ke tafiya yadda ya kamata. Ta ce jarin da kasar Sin ke zubawa a Afirka, musamman a fannin inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a, na karfafawa kasashen Afirka gwiwar samun sabon ci gaba.
Yayin da take tsokaci kan batutuwan da ya kamata a maida hankali kai yayin da ake hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, Ahunna ta yi kira da a kara hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da bukatun kasashe da yankunan Afirka daban-daban, ta yadda za'a kara samun sakamako mai kyau bisa hadin-gwiwar moriyar juna.(Murtala Zhang)