in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma ta samar da kyakkyawar makoma ga jama'ar kasar Uganda
2018-08-30 10:38:22 cri

A gun taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a watan Disamba na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da inganta sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Afirka zuwa dangantakar abokantaka dake tsakaninsu a dukkan fannoni, kana ya gabatar da shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin masana'antu, aikin noma, ayyukan more rayuwa, hada-hadar kudi, samun bunkasuwa tare da gurbata yanayi ba, samar da sauki ga ciniki da zuba jari, yaki da talauci, kiwon lafiya, al'adu, kiyaye zaman lafiya da tsaro da sauransu, wadanda aka tsara taswirar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tare da bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a tarihi.

A gabannin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a nan birnin Beijing, za mu yi muku bayani kan sabon ci gaban da aka samu a fannin ayyukan more rayuwa yayin da sassan biyu suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu.

A karshen kogin White Nile dake tebkin Victoria na birnin Kiryandongo na arewacin kasar Uganda, masanan kamfani na 8 na samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin, da ma'aikatan kamfanin dake wurin, suna kokarin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma a mataki na karshe, aikin da ya kasance mafi girma a wannan fanni a tarihin kasar.

An fara gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma a watan Disamba na shekarar 2013, bisa jarin kashi 15 cikin dari da gwamnatin kasar Uganda ta zuba, da kuma kashi 85 cikin dari da bankin shige da fice na kasar Sin ya samar da rancen kudi. Ana sa ran za a kammala gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa din a karshen shekarar bana wato shekarar 2018, tare da fara samar da wutar lantarki a hukunce, ta haka za ta kasance tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa mafi girma a yankin gabashin Afirka.

Kasar Uganda tana daya daga cikin kasashen da kowane dan kasar ke yi amfani da wutar lantarki mafi karanci a duniya. Yawan wutar lantarkin da mutanen biranen kasar Uganda bai wuce kashi 40 cikin dari bisa na adadin 'yan kasar ba, kuma yawan ta ga mutanen kauyukan kasar bai wuce kashi 6 cikin dari kacal ba. Haka kuma farashin wutar lantarki na kasar ya yi tsada, har ma mutane da dama na kasar ba su iya sabawa da shi, ta hakan an rage bukatun yin amfani da wutar lantarki na jama'ar kasar.

A hakika dai, kasar Uganda tana da fifikon albarkatu a fannin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. Manajan mai kula da aikin tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma Deng Changyi ya yi bayani cewa, a sakamakon sauri da yawan ruwan kogin Nile ba tare da samun babban canji ba, kana ba shi da lokacin cikar kogi da kuma lokacin kafewar kogi, ta haka ana iya samar da wutar lantarki ta karfin ruwan kogin yadda ya kamata ba tare da yin la'akari da lokacin kogin ba.

Deng Changyi ya bayyana cewa,"Aikin tashar samar da wutar lantarki ta Karuma, aiki ne mafi muhimmanci da shugabannin kasashen Sin da Uganda suka sa kaimi ga gudanar da shi, wanda zai sa kaimi ga cimma burin kasar Uganda na samun ci gaba da wadata a kasar. Shugabannin kasashen biyu sun sa lura sosai kan aikin, kuma wannan muhimmin aiki ne dake cikin shirin samun bunkasuwa na shekarar 2040 na kasar Uganda."

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Uganda UEGCL, yana daya daga cikin kamfanoni masu gudanar da ayyuka a Karuma. Manaja mai kula da harkokin hadin gwiwa na kamfanin Simon Kasyate ya bayyana cewa, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin, abokin hadin gwiwa ne mai kyau a fannonin gudanar da ayyuka da horar da ma'aikata.

Simon ya bayyana cewa, "Yayin da ake gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, wadda yawanta ya kai megawatt 600, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin yana son sauraron ra'ayoyinmu, da gyara shirin bisa hali mai dacewa, wanda hakan ke nuna kamfanin na daukar alhakin dake wuyansa. Mun yi imanin cewa, za a gama wannan aiki mai inganci yadda ya kamata bisa lokacin da aka tsara. Hakazalika kuma, kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya taimakawa kamfanonin samar da wutar lantarki na kasar Uganda wajen inganta karfinsu, musamman horar da ma'aikata a wannan fanni. A ganina wannan yana da muhimmanci sosai, domin bayan da aka gama aikin, ma'aikatanmu za su iya tabbatar da gudanar da ayyukan tashar samar da wutar lantarki yadda ya kamata. Ina tsammanin cewa, aikin Karuma zai kasance aiki mafi kyau a tarihin ayyukan gine-gine na kasar Uganda, za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Uganda da Sin a fannin fasahohi na zamani, da kirkire-kirkire bayan da aka gama wannan aiki." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China