in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan Amurka kan birnin Kudus da 'yan gudun hijirar Falasdinu za su rusa zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya
2018-08-30 10:28:36 cri

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, ya yi gargadin cewa, matakan da Amurka ta dauka kan birnin Kudus da kuma 'yan gudun hijirar Falasdinu, za su wargaza shirye-shiryen zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mahmoud Abbas ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Ramallah, tare da Bakir Izetbegovic, jagoran shugabanin Bosnia da Herzegovina.

Ya ce, wadancan matakai sun sa Amurka ta zama mai nuna bangaranci, sannan ba ta cancanci daukar nauyin tattaunawar samar da zaman lafiya ba.

A watan Fabrerun da ya gabata ne Mahmoud Abbas ya gabatar da wani shirin zaman lafiya ga kwamitin sulhu na MDD, yana mai kira da a gudanar da taron tattaunawar zaman lafiya na kasa da kasa da kuma samar da wata dabara da ta kunshi kasashen duniya domin daukar nauyin shirin.

Shirin na shugaba Abbas ya kunshi samar da kasashe 2 da za su dace da iyakokin da aka shata a 1967, tare da ba Falasdinawa 'yancin cin kashin kai da mayar da gabashin birnin Kudus matsayin babban birninsu.

A nasa bangaren, Bakir Izetbegovic, ya tabbatar da cewa, kasarsa ta kada kuri'ar amincewa da manufofin kare Falasdinawa fararen hula da kuma yankunan Falasdinu.

Ya kuma jaddada kiran da kasarsa ta yi na kawo karshen rikici da fara tattaunawa domin neman zaman lafiya a yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China