in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin FOCAC na Beijing sabon ci gaba ne na hadin gwiwar Sin da Afrika
2018-08-30 10:16:49 cri

Taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC wanda za a gudanar a Beijing a wata mai zuwa zai kasance a matsayin muhimmin al'amari da zai kara daga matsayin hadin gwiwar Sin da Afrika, da kuma karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Morocco, in ji jakadan Sin a kasar Morocco, Li Li, a wata tattaunawa ta baya bayan nan.

Kasar Sin da kasashen Afrika suna fuskantar wasu damammaki da kalubalolin ci gaba tare, Li ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. A yayin da za'a gudanar da taron kolin Beijing a ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumba, shugabannin Sin da na Afrika za su tattauna game da hanyoyin da za su tabbatar da bunkasa ci gaban dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Zai kasance wani sabon ci gaba ne na hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika, in ji jakadan.

A shekarar 2017, a lokacin ziyararsa a kasar Sin, ministan harkokin wajen kasar Morocco Nasser Bourita, ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don bunkasa ci gaban shawarar ziri daya da hanya daya. Morocco ita ce kasa ta farko daga yankin Larabawa da ta kulla irin wannan dangantaka da Sin.

Li ya ce, shawarar za ta samar da kyakkyawar dama ga ci gaban dangantakar Sin da Morocco, wadda daya ne daga cikin muhimman bangarori na karfafa alakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa.

Li ya ce, damammakin kyautata huldar ciniki tsakanin Sin da Morocco yana da girman gaske, a lokacin da kamfanonin hada motoci na Morocco, da na sufurin jiragen sama, da masaku suke kokarin shiga wani sabon matakin ci gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China