in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: Lalubo sabbin dabarun shiga tsakani wajen warware rikici ya zama wajibi
2018-08-30 09:57:45 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce tunanin sabbin dabarun shiga tsakani wajen warware rikice-rikice abu ne da ya zama wajibi.

Antonio Guterres ya bayyana yayin wani taron muhawara na kwamitin sulhu na majalisar mai taken "Kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya: shiga tsakani da warware rikice-rikice cikin lumana" cewa, yayin da salon rikice-rikice ke sauyawa, ya kamata fahimtar abubuwan da suka kunshi ingantaccen aikin shiga tsakani su sauya, yana mai cewa tunanin sabbin dabaru ba zabi ba ne, abu ne da ya zama wajibi.

A cewar wani daftari da Birtaniya, wadda ke shugabantar kwamitin a wannan watan ta raba, manufar muhawarar ita ce, samarwa mambobin kwamitin damar nazarin rawar da MDD ke takawa wajen jagoranta da goyon bayan kokarin shiga tsakani da yadda za a karfafa ta da kuma yadda kwamitin tsaron da mambobinsa za su mara baya ga yunkurin.

Ya kara da cewa, cikakkun yarjejeniyoyin zaman lafiya na kara wuyar samu, sannan ba sa dorewa. Haka zalika kudurin shugabanci na gari ya yi karanci, kana hankalin al'ummar duniya ya karkata.

A don haka, sakatare janar din ya bukaci da a kara amfani da ayyukan shiga tsakani a matsayin hanyar ceto da inganta rayuwar miliyoyin al'umma a fadin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China