Shugaban Botswana, Mokgweetsi Masisi, ya baro kasarsa a jiya Laraba, domin ziyarar aiki da halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika da za a yi a nan birnin Beijing na kasar Sin.
Da yake ganawa da manema labarai jiya a birnin Gaborone, mukadashin ministan harkokin wajen kasar Nonofo Molefhi, ya ce a matsayin Sin na kasa mai tasowa da ta samu ci gaba, ta kuduri niyyar karfafa dangantaka da kasashen Afrika domin kara taimaka musu, ta fuskar raya tattalin arziki da kyautata zamantakewa.
Ya ce, Botswana da kasar Sin na da hadin gwiwa a fannonin da suka shafi kiwon lafiya da gine-gine da saura abubuwan ci gaba, don haka, halartar taron FOCAC zai taimakawa kasashen biyu kara karfafa alakarsu.
Ya kara da cewa, taron zai ba kasashen Afrika dake da muradin bunkasa kansu, kyakkyawar dama ta morar kasar Sin ta hanyar koyon dabaru mabanbanta da ta yi amfani da su wajen samun ci gaba da inganta rayuwar al'ummarta. (Fa'iza Mustapha)