Liu Hongwu ya bayyanawa 'yan jarida a wannan rana cewa, taron koli na Beijing na bana zai waiwayi ayyukan da aka gudanar bayan da aka kafa dandalin tattaunawar na FOCAC a cikin shekaru 18 da suka gabata, kana za a gabatar da shiri na raya Sin da Afirka na shekaru 3 masu zuwa har ma na tsawon lokaci, ta haka za a inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi.
Liu Hongwu ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da tsarin hadin gwiwa na kasa da kasa kamar shawarar "ziri daya da hanya daya", hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashe membobin kungiyar BRICS zasu taimaka wajen cimma samun moriyar juna ta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka tare da inganta hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)