Kakakin MDD ya sanar cewa, wakilin musamman na MDD kan rikicin Syria ya gayyaci kasashen duniya masu yawa domin sun halarci taron tuntubar juna a ofishin MDDr dake Geneva a ranar 14 ga watan Satumba.
Wakilin musamman na MDD a Syria, Staffan de Mistura, ya gayyaci kasashen Masar, Faransa, Jamus, Jordan, Saudi Arabia, Birtaniya da kuma Amurka domin tattaunawar dake tafe, Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana hakan a taron manema labarai.
Wakilin musamman na MDD yana son yin amfani da wannan damar ce don tattaunawa tare da manyan wakilan wadannan kasashen game da matakai na gaba da za'a dauka domin warware rikicin kasar wanda kwamitin sulhun MDD mai lamba 2254 ya cimma matsaya kansa a shekarar 2015, wanda ya kunshi yunkurin MDDr wajen kafa kwamitin tsara kundin tsarin mulkin kasar Syria, da kuma daukar manyan hanyoyin tabbatar da shirin, in ji Dujarric.(Ahmad Fagam)