in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance babbar abokiyar huldar ciniki ta Afrika cikin shekaru 9 a jere
2018-08-29 10:51:55 cri

Wata kididdigar ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ta nuna cewa, Sin ta kasance babbar abokiyar huldar cinikayya ta kasashen Afrika a cikin shekaru tara a jere, lamarin da ya kara ingiza hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar kasuwanci.

An samu bunkasuwar harkokin cinikayya tsakanin Sin da Afrika tun bayan kaddamar da manyan yarjejeniyoyin hadin gwiwa 10 shekaru uku da suka gabata. A watanni shidan farkon shekarar nan ta 2018, mu'amalar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ya karu da kashi 16 bisa 100 idan aka kwanta da makamancin lokacin bara wanda ta tasamma dala biliyan 98.8, Qian Keming, mataimakin ministan cinikin kasar Sin ne ya tabbatar da hakan a taron manema labarai.

Kasar Sin ta sanar da kafa tsare tsaren hadin gwiwa 10 karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika a taron kolin Johannesburg na hadin kan Sin da Afrika (FOCAC) a shekarar 2015, kuma mafi yawa daga cikinsu sun shafi batun tattalin arziki ne da cinikayya.

Qian ya ce, kusan dukkan yarjejeniyoyin da suka shafi ciniki da tattalin arziki, an riga an aiwatar da su kuma da dama daga cikinsu sun ba da kyakkyawan sakamako.

A shekaru uku da suka gabata, kasar Sin ta zuba jarin kai tsaye a nahiyar Afrika da ya kai dala biliyan 3, kana ana samun ci gaba sosai a fannin hadin gwiwar kere-kere, harkokin kudi, yawon shakatawa, da harkar sufurin jiragen sama.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China