1. A ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2017, wato ranar musamman da aka kebe a matsayin bikin mata na duniya, an sa dukkan ma'aikata mata na ofishinmu dake kula da wani bangare na aikin shimfida layin dogo a kasar Kenya, zuwa wani wuri mai ni'ima da ake kira "Tsavo National Park".
2. Muhallin wurin na da kyan gani sosai. Sai dai a lokacin da muke daukar hoto, wayar salulata ta fadi cikin ruwa.
3. Ko da yake ruwan ba shi da zurfi, amma mun kasa dauko waya ta daga cikin ruwan, saboda an ce akwai kada a cikin ruwa, abin da ya ba mu tsoro.
4. Mun gwada wasu dabaru amma mun kasa. Sa'an nan direban kamfaninmu Lucas ya fito, ya tafi zuwa bakin ruwa sannu a hankali.
5. Masu gadi sun shirya bindigoginsu, suna duba ruwan kogin. Za su bude wuta idan wata kada ta fito.
6. Bayan da ya dawo, kowa ya yi murna sosai. Na tarbe shi cikin zumudi, na ce, "Lalle kai jarumi ne!" Ya mayar mana da wayata, yana murmushi saboda jin kunya. Daga bisani, mun kulla zumunci tsakaninmu. (Bello Wang)