in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar "Ziri daya da Hanya daya" Ta Samar Da Wata Sabuwar Hanya Ga Kokarin Sauya Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
2018-08-28 20:28:15 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya gabatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" a shekarar 2013. Sa'an nan a yayin taron karawa juna sani da aka kira a birnin Beijing na kasar Sin don tunawa da cika shekaru 5 da kaddamar da shawarar, shugaban ya ce, shawarar "Ziri daya da Hanya daya" ta dace da bukatar da ke akwai ta sauya tsare-tsaren tafiyar da duniyarmu, haka kuma ta samar da wata sabuwar hanyar da za a iya bi wajen gudanar da sauye-sauye a wannan fanni.

Kalaman shugaban sun nuna ma'anar shawarar "Ziri daya da Hanya daya", wato za ta taimaka ga hadin gwiwar Sin da sauran kasashe a fannin tattalin arziki, haka kuma za ta kara azama ga yunkurin sauya tsarin tafiyar da harkokin duniya, gami da tabbatar da kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama. Hakika, lokacin da aka gabatar da shawarar shekaru 5 da suka wuce, watakila ba a fahimci muhimmancinta sosai ba.

Amma kawo yanzu, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100 sun shiga shawarar, kana kudin cinikayyar kayayyakin da kasar Sin ta yi da wadannan kasashe ya zarce dalar Amurka biliyan 5000. Sa'an nan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje bisa tsarin shawarar ya zarce dala biliyan 60, baya ga guraben aikin yi fiye da dubu 200 da aka samar a kasashen. Babban fa'idar dake tattare da shawarar ya sa babban taron MDD, da kwamitin sulhunta suka rubuta shawarar cikin kundurinsu.

A nasa bangare, Martin Jacques, farfesa na jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya, ya ce kasar Sin ta janyo hankalin kasashe da yawa, domin suna kallon kasar Sin a matsayin wata kasa dake samar da "sabuwar dama". Wannan sabuwar dama ita ce ra'ayin da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" ta gabatar na "tattaunawa tare, da raya harka tare, gami da raba moriya".

Yanzu duniyarmu na fuskantar wasu matsaloli, ga misali, tsanantar yakin ciniki da ake yi, da yanayin koma baya da tsarin dunkulewar kasashe daban daban a waje guda da ake fama da shi, yanayin da ya nuna cewa tsohon tsarin tafiyar da duniya ya kasa biyan bukatun da suke kunno kai wajen tinkarar sauyin yanayi na fannonin siyasa da tattalin arziki. To, ina bil Adama za su shiga? Mece ce mafiya? Ta yaya za a daidaita matsalolin da ake fuskanta a fannonin tabbatar da zaman lafiya, da raya tattalin arziki, gami da tafiyar da harkokin kasa? ... Dangane da jerin wadannan tambayoyi, za a iya samun amsoshinsu cikin ra'ayin "tattauna tare, da raya harka tare, gami da raba moriya".

"Tattauna tare", wato bangarori daban daban su tattauna kan harkokin dake gabansu, a maimakon bin umurnin wani ko wata, lamarin da ya nuna ka'idar "adalci" wajen aiwatar da harkokin kasa da kasa. A halin yanzu, kasashe masu tasowa suna bukatar raya harkokin masana'antu, samun 'yanci a fannin tattalin arziki da kuma neman ci gaban kasashensu baki daya, amma ba su samu cikakken goyon baya ba sakamakon ikon da yammacin kasashen duniya ke nunawa kan manufofin kasa da kasa, da kuma karfin fada a ji a kan asusun ba da lamuni na IMF da bankin duniya da sauran hukumomi makamanta.

Kasar Sin ta fito da kiran "Ziri daya da hanya daya", inda ta karfafa manufar yin tattaunawa cikin hadin gwiwa, kafa bankin zuba jari kan gina ababen more rayuwa na Asiya, da kuma asusun hanyar siliki da dai sauransu, domin raya kasashen dake kan hanyar siliki, da kuma samun goyon baya daga gamayyar kasa da kasa cikin yanayi na adalci.

"Raya harka tare", wato bangarori daban daban su gudanar da ayyuka cikin hadin gwiwa, lamari ne da ya nuna ka'idar "bude kofa ga waje" wajen aiwatar da harkokin kasa da kasa. Cikin shekaru biyar da suka gabata, kasashen yammacin duniya sun sha illata shirin "ziri daya da hanya daya", amma a hakika, shirin ya sada zumunta a tsakanin bangarori daban daban. Shirin ya kuma dace da shirin "kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya" da kasar Rasha ta fidda, shirin "yin musaya a tsakanin bangarori daban daban" da kungiyar kasashen dake kudu maso gabashin Asiya ta samar, da kuma "shirin raya kasa nan da shekarar 2030" da kasar Saudiya ta fito da shi da sauran makamantansu. Haka kuma, manyan ayyukan da aka yi da suka hada da layin jiragen kasa tsakanin Sin da kasashen Turai, tashar jiragen ruwa ta Piraeus ta kasar Greece, da kuma babban yankin masana'antu na Sin da Belarus da dai sauransu sun ba taimaka kwarai da gaske ga al'ummomin Sin da sauran kasashen da abin ya shafa.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kiran shiga shawarar "Ziri daya da hanya daya" da aka yi shi ne kiran hadin gwiwar tattalin arziki, ba kawance na siyasa ko na soja ba, ya yi kira da a bude kofa ga waje, kuma kasar Sin tana maraba da duk wanda yake son shiga wannan shiri. Tabbas ba zai dace da manufar wasu kasashen dake son mallake harkokin kasa da kasa ba.

"Raba moriya", wato bangarori daban daban za su more sakamakon ci gaba da aka samu a maimakon wanda ya yi nasara shi kadai ya cinye sakamakon ci gaba, wannan ya yi cikakken bayani game da kalmar "kawo moriya ga kowa da kowa" a lokacin da ake tafiyar da mulkin duniya yanzu. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sha bayyana cewa, kasar Sin ce ta bullo da shawarar "ziri daya da hanya daya", amma duk duniya ne za su ci gajiyar damammaki da sakamako daga shawarar. A cikin wani jawabin da ya gabatar kwanan baya, shugaba Xi Jinping ya sake jaddada cewa, za a kara mai da hankali kan ayyukan more rayuwar al'umma da ake bukata cikin gaggawa domin al'ummomin fararen hula su ci gajiya sosai, ta yadda za a iya kawo alheri kamar yadda ya kamata ga al'ummomin kasashen da shawarar ta shafa a lokacin da ake karfafa aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" nan gaba. Sannan dole ne a yi watsi da tunanin "bangare daya ne ke samun riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hasara" kwata kwata.

A cikin shekaru 5 da suka gabata, ayyukan da aka samar bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" ba ma kawai sun ciyar da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ba, har ma sun ba da damar lalubo sabbin dabarun da suka dace na kyautata aikin tafiyar da harkokin kasa da kasa. Amma mene ne sabon matakin da za a dauka nan gaba? Xi Jinping ya nuna cewa, dole ne a sauya hanyoyin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" domin kokarin samar da karin ayyuka masu inganci tare da samun sakamakon a zo a gani. Muddin duk wanda ya tsaya tsayin daka wajen bin ka'idodin "tattaunawa tare, da raya harka tare, gami da raba moriya", tabbas shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta kawo wa duk duniya da al'ummomin kasa da kasa karin sakamakon da ya dace, har ma za ta kawo karin dabarun kyautata aikin tafiyar da harkokin kasa da kasa. Sakamakon haka, tabbas duk wasu maganganun da wasu kasashen yammacin duniya suke furtawa kan shawarar, magana ce ta banza kawai. (Marubuciya: Sheng Yuhong, ma'aikaciyar cibiyar tattara labaru ta CRI; Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China