in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Cote d'Ivoire
2018-08-28 20:16:04 cri
A yau ne mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Cote d'Ivoire, Marcel AMON-TANOH, a birnin Beijing na kasar Sin Yayin ganawar tasu, jami'in na kasar Sin ya ce, kasarsa tana maraba da zuwan shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara kasar Sin don halartar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC da za a gudanar a birnin Beijing a mako mai zuwa. Ta la'akari da shirin kasashen Sin da Cote d'Ivoire na kulla yarjejeniyar shiga shawarar "Ziri daya da Hanya daya", kasar Sin na son yin amfani da wannan dama don karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2, tare da tabbatar da moriyarsu ta bai daya, gami da nahiyar Afirka, har ma da sauran kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Cote d'Ivoire, ya ce hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Cote d'Ivoire da Sin ya kasance abin koyi. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China