Jami'in ya kara da cewa, sabbin matakan da za a dauka za a hade su da shawarar "Ziri daya da Hanya daya", da ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063 da kungiyar tarayyar Afirka AU ta gabatar, da ajandar samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 ta MDD, gami da tsare-tsaren raya kasa na kasashe daban daban dake nahiyar Afirka. (Bello Wang)