in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummun duniya za su ci gajiyar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2018-08-28 10:45:23 cri

Za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumba a nan birnin Beijing, taron dake da taken: "hadin gwiwa domin samun moriyar juna, sanya kokari domin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka".

Tsohon wakilin musamman kan harkokin Afirka na gwamnatin kasar Sin, kuma tsohon jakadan kasar Sin dake wakilci a Zimbabwe, da Afirka ta Kudu Liu Guijin, ya gaya wa wakilinmu cewa, a karkashin yanayin da ake ciki yanzu, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai amfanin al'ummun sassan biyu, haka kuma zai amfanin daukacin al'ummun kasashen duniya, tare kuma da taka rawa kan aikin gina kyakkyawar makomar bil Adama a fadin duniya.

Domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, tare kuma da dakile kalubale da ingiza ci gaba, an gudanar da taron ministocin kasashen da suka shiga dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka karo na farko a watan Oktoban shekarar 2000 a nan birnin Beijing, taron da ya samu halartar ministoci sama da 80, wadanda suka zo daga kasar Sin da kasashen Afirka 44, da wasu wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da kuma na shiyya shiyya da abin ya shafa.

Kan wannan, tsohon wakilin musamman kan harkokin Afirka na gwamnatin kasar Sin, kuma tsohon jakadan kasar Sin dake wakilci a Zimbabwe da Afirka ta Kudu Liu Guijin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 18 da suka gabata, wato tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu, sannu a hankali dandalin ya riga ya kasance muhimmin dandalin da ke sa kaimi kan ci gaban Sin da Afirka, yana mai cewa, "Tun bayan da aka kafa dandalin, huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta samu kyautatuwa a bayyane. Ko shakka babu dandalin ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban huldar sassan."

Kasar Sin kasa ce mafi girma mai tasowa, kuma yawancin kasashen dake nahiyar Afirka kasashe ne masu tasowa, don haka ya dace sassan biyu su yi amfani da dandalin, su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, ta yadda za su samu ci gaba tare. Tun daga shekarar 2000 har zuwa shekarar 2008, adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka na karuwa da kaso 34 bisa dari a kowace shekara, daga baya wato tun daga shekarar 2009, kasar Sin ta zamo kasa mafi girma wadda ke gudanar da cinikayya da kasashen Afirka, a maimakon kasar Amurka. Bisa alkaluman da aka fitar a wannan wata, a shekarar 2017, gaba daya adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka ya zarta dalar Amurka biliyan 163.

Yayin taron kolin dandalin da aka gudana a birnin Johannesburg na kasar ta Afirka ta Kudu a shekarar 2015, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za ta aiwatar da shirinta na raya kasashen Afirka a fannoni goma. Liu Guijin ya kara da cewa, taron kolin dake tafe zai kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, yana mai cewa, "Misali a fannin samar da kayayyaki, ina fatan sassan biyu za su kara daukan matakai da za su dace, domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a yayin wannan taron kolin da za a gudanar, dalilin da ya sa haka shi ne, kasashen Afirka ba su samu ci gaba sosai ba a fannin masana'antu, amma kasar Sin ta nuna fifikonta wajen samar da kayayyaki, a don haka kasar Sin tana iya taimakawa kasashen Afirka, wajen zamanintar da masana'antunsu."

Kana Liu Guijin yana ganin cewa, sassan biyu suna iya kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da yaki da talauci, da raya aikin gona da sauransu. Ko shakka ba bu hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka yana da makoma mai haske, saboda suna iya samun moriyar juna ta hanyar gudanar da hadin gwiwa. Yana mai cewa, "Sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwa ne bisa tushen moriyar juna, kuma idan aka iya cimma burin samun moriyar juna, cikin sauki za a iya gudanar da hadin gwiwa, tare kuma da samun makoma mai haske. Kana ba abu ne mai yiwuwa ba, a haifar da wata illa ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka."

Babban taken taron kolin shi ne: "hadin gwiwa domin samun moriyar juna, sanya kokari domin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka", Liu Guijin ya bayyana cewa, yanzu wasu kasashe suna ba da kariya ga cinikayyar kasashensu, domin yaki da ka'ida, kamata ya yi kasashen Sin da Afirka su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Ya ce, "Ba ma kawai lamarin zai amfanin kasar Sin da kasashen Afirka ba ne kadai, har ma zai amfanin sauran kasashen duniya, tare kuma da taka rawa ga aikin gina kyakkyawar makomar bil Adama, saboda kasashe a fadin duniya suna dogaro ga juna, don haka ba zai yiwu wata kasa daya ta samu ci gaba bisa karfin kanta kadai ba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China