in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zumunci tsakanin Sin da Afirka a idon Xi
2018-08-27 11:09:48 cri

Kasar Sin da kasashen Afirka suna da dadadden zumuncin tsakaninsu, a don haka suna goyon bayan juna, suna taimakawa juna a ko da yaushe, yau ga wasu labarai da abokiyar aikinmu Jamila ta hada mana kan zumuncin dake tsakanin sassan biyu a idon shugaban kasar Sin Xi Jinping.

A watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a wasu kasashen Afirka karo na farko, tun bayan da ya fara rike da mulkinsa a kasar ta Sin, yayin da yake gabatar da wani jawabi a majalisar dokokin jamhuriyar kasar Kongo, ya bayyana wani labari game da zumunci mai zurfi dake tsakanin al'ummun kasar Sin da kasashen Afirka, yana mai cewa, "A watan Aflilun shekarar 2014, bala'in girgizar kasa mai tsanani ya auku a yankin Yushu na lardin Qinghai na kasar Sin, gwamnatin jamhuriyar kasar Kongo ta samar da tallafin kudi domin gina wata makarantar firamare a yankin da bala'in ya auku, shugaban kasar Denis Sassou-Nguesso ya sanyawa makarantar suna 'makarantar firamare ta zumuncin Sin da Kongo'. Yanzu yaran yankin Yushu suna karatu a cikin sabbin dakunan makarantar, suna gudu suna wasa a kan sabon filin wasan da aka gina, domin nuna babbar godiya ga shugaba Sassou-Nguesso, daliban makarantar sun rubuta masa wata wasika, inda suka bayyana cewa, tsuntsaye suna jin dadin walwala a cikin sararin samaniya mai fadi, dawaki suna kara karfin jiki saboda samar musu filin ciyayi, furanni suna kara kyan gani bisa dalilin isasshen hasken rana da ruwan sama, zaman rayuwarmu ya kara kyautata saboda tallafin da gwamnati da al'ummar kasar Kongo suke samar mana."

Duk da cewa, kudin gina wata makarantar firamare ba shi da yawa, amma jamhuriyar Kongo wadda ke da al'ummun miliyan 3 kacal, ita kanta tana fama da talauci mai tsanani, a karkashin irin yanayin ta, shugaba Sassou-Nguesso ya tsai da kudurin samar da tallafin kudin Sin yuan miliyan 16, domin gina wata makarantar firamare ta zamani wadda take iya daukar dalibai 240 a yankin Yushu na kasar Sin, bayan yankin ya sha fama da hasara sanadiyyar aukuwar bala'in girgizar kasa.

Kana shugaba Xi ya gabatar da wani labari daban game da Sinawa 3 dake Kongo sun ceto makwabtansu guda 12, a cewarsa: "A daren wata rana a watan Disamban shekarar 2012, ba zato ba tsammani, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a Brazzaville, fadar mulkin jamhuriyar Kongo, har ruwan saman ya rushe gidajen kwana da dama a karkarar birnin, Sinawa dake sauka a wurin sun riga sun tsira rayukan su daga hadarin, amma lokacin suka tarar da cewa, makwabtansu ba su gano hadarin da suke fuskanta ba, sai suka tsunduma cikin ruwa suka yi iyo zuwa gidajensu, suka ceto makwabtan na su 12 cikin nasara, wadanda a cikinsu, har da yara guda 5, lamarin da ya burge mazauna wurin matuka."

Ban da haka kuma shugaba Xi Jinping ya kara bayyana wani labari game da kaunar da samarin kasar Sin suke nunawa ga nahiyar Afirka.

A ranar 25 ga watan Maris na shekarar 2013, shugaba Xi ya gabatar da wani jawabi a cibiyar taron kasa da kasa ta Julius Nyerere dake kasar Tanzaniya, inda ya bayyana cewa, "Na ji an ce, wani saurayi da wata budurwa 'yar kasar Sin sun fahimci yanayin da kasashen Afirka ke ciki sosai ta hanyar kallon telibijin, har sun sa niyyar zuwa nahiyar domin kallon ni'imtattun wurare da idonsu, daga baya sun yi aure, sun tsai da kudurin mayar da Tanzaniya a matsayin wurin nishadin watan zumarsu, wato watan farko bayan aurensu, da suka isa kasar, sai suka ziyarci filin ciyayi na Serengeti, inda suka ji dadi sosai. Bayan da suka komo kasar Sin, sun rubuta wasu bayanai da dama game da ziyararsu a Tanzaniya. Sun shigar da bayanai da hotunan da suka dauka kan shafin yanar gizo, saboda bayanan suna da ban sha'awa, shi ya sa masu shiga yanar gizo da yawan gaske ke karanta bayanan, har ma suka nuna yabo gare su. Ango da amarya sun bayyana cewa, tabbas suna kaunar Afirka, kuma har abada ba za su manta da nahiyar ba. Labarin ya nuna cewa, al'ummun kasashen Sin da Afirka suna da dadadden zumunci dake tsakaninsu. Kuma muddin dai sassan biyu sun kara karfafa cudanya tsakaninsu, zumuncin dake tsakaninsu zai kara zurfafa sannu a hankali."

Da idonsa, shugaba Xi ya ga zumuncin. Ya kan bayyana cewa, zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka yana da dogon tarihi, duk da cewa, yanayin da kasashen duniya ke ciki ya hadu da manyan sauye-sauye, amma har abada zumunci da aminci dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka ba zai sauya ba. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China