in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta wallafa ka'idojin ladaftarwa
2018-08-27 10:40:18 cri

Kwamitin koli na JKS, ya wallafa ka'idojin ladaftarwa 142 da aka yiwa gyare gyare, wadanda kuma kwamitin ya ba da umarnin aiwatar da su yadda ya kamata.

Wata takardar umarnin aiwatarwa da kwamitin ya fitar, ta ce an kaddamar da dokokin ne a karfon farko cikin watan Oktoban shekarar 2015, domin su taka rawar gani wajen aiwatar da tanaje tanajen dake kunshe cikin kundin tsarin jam'iyyar, da ma sauran dokoki da suka jibanci ayyukan jam'iyyun kasar. Kaza lika dokokin na kare hurumin dokokin ladftarwa, da na ayyukan jam'iyyun bisa ka'idojin doka.

Takardar bayanin ta kara da cewa, an gudanar da gyaran ne bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar karo na 19, wanda ya maida hankali ga aikin ladaftarwa, a matsayin ginshikin ginin jam'iyya a sabon zamani, ya kuma kunshi matakai na tabbatar da nasarar aiwatar da da'a wajen aiwatar da tanajin kundin tsarin jam'iyyar.

Ka'idojin dai sun hade dabarun aiwatar da tunanin shugaba Xi Jinping, game da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na Sin a sabon zamanin da ake ciki, da kuma ruhin taron wakilan JKS karo na 19 da ya gabata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China