Kakakin ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayar da wani dan jarida ya yi masa, inda aka yi tambaya cewa, kasar Amurka ta ce, wai kasar Sin ta canza ra'ayinta dangane da batun nukiliya na zirin Koriya, lamarin da ya yi tasiri kan yunkurin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa na daidaita batun nukiliya ta hanyar shawarwari, dangane da maganar, mene ne ra'ayin kasar Sin?
Game da wannan tambaya, kakakin kasar Sin ya amsa cewa, zancen bangaren Amurka ya saba da hakikanin yanayin da ake ciki, wanda ya nuna kasar ba ta kula da sauran kasashe ba. Zancen ya sa kasar Sin ta nuna damuwa sosai, kuma ta riga ta nuna rashin jin dadi ga kasar Amurka.(Bello Wang)