in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce har yanzu kungiyar IS babbar kalubale ce
2018-08-24 11:15:55 cri
Mataimakin Sakatare Janar na MDD mai kula da ofishin yaki da ta'addanci na Majalisar, Vladimir Voronkov, ya ce duk da gaggarumin asarar da IS ta yi, har yanzu tana ci gaba da zama babbar abun damuwa.

Vladimir Voronko ya bayyanawa kwamitin sulhu na MDD cewa, tun daga karshen 2017, ake cin nasara kan IS a Iraqi, sannan karfinta na raguwa a Syria.

Da yake yi wa kwamitin bayani game da rahoton Sakatare Janar na Majalisar kan kungiyar IS, jami'in ya ce an yi kiyasin kungiyar na da mambobi sama da 20,000 a Iraqi da Syria. Kuma daga cikinsu, wasu na yaki ne da jami'an tsaro yayin da wasu ke shiga yankuna da birane. Haka kuma, kungiyar ta rarraba tsarin shugabancinta, domin rage asarar da ta yi.

Har ila yau, ya ce akwai yiwuar IS ta ci gaba da yin tasiri a Iraqi cikin matsakaicin lokaci, saboda rikicin dake akwai da kuma wuyar dake tattare da kalubalen tabbatar da zaman lafiya. Baya ga haka, ya ce akwai wasu da suka yi wa kungiyar mubaya'a a Afghanistan da kudu maso gabashin Asia da yammacin Afrika da Libya, da kuma wani adadi kalilan a Sinai da Yemen da Somalia da kuma yankin Sahel.

Vladimir Voronko ya kara da cewa, kalubalen dake tattare da komawa da sake samun wajen zama ga mayakan na kasashen waje babba ne.

Ya ce kwararar mayakan kasashen waje a Iraqi da Syria ya tsaya cik. Sai dai kuma komawarsu, duk da a hankali suke yi, babbar barazana ce.

Bugu da kari, ya ce karuwar barazanar mayakan IS a duniya musammam mayakan na wasu kasashe zai zama mai wuyar fassara. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China