in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberiya: Mutane 9 ake fargabar sun mutu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife
2018-08-24 09:29:07 cri
Mahukuntan kasar Liberiya sun tabbatar da cewa, mutane 9 ne ake fargabar sun gamu da ajalinsu, bayan da wani kwale-kwale mai dauke da mutane 15 ya kife a garin Dolo dake tsakiyar yankin Margibi.

Safuritandan yankin na Margibi Jerry Varnie ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya zuwa yanzu masu aikin ceto sun yi nasarar ceto mutane 6 da suka fada cikin kogi a ranar Laraba da rana.

Hadarin ya faru ne lokacin da mutanen dake cikin kwale-kwalen galibinsu dalibai suka isa Manawhala, wurin da za a tsallaka zuwa yankin Lower Margibi. Dalibin dai za su tsallaka kogin Gben ne don su yi rijistar jarabawar shekarar karatu dake tafe.

A nasa martani kan hadarin da ya faru, magajin garin hadin gwiwa Samuel Berrien, ya ce jami'an shararren wurin dake yankin na Margibi, sun ba da umarni rufe dukkan wuraren tsallakawa dake kusa da birnin har zuwa karshen lokacin bazara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China