in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Aikin asibitin Peace Ark ya nuna halin jin kai
2018-08-23 18:43:32 cri

Yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, aikin jinya kyauta da asibitin tafi da gidanka na sojojin ruwan kasar Sin wato "Peace Ark" ke gudanarwa, a kasashe hudu wato Papua New Guinea, da Vanuatu, da Fiji da Tonga dake kan yankin tekun Pasifik, ya nuna wa al'ummun kasashen duniya halin jin kai na kasa da kasa, da manufofin diplomasiyar "zaman lafiya da ci gaba, da hadin gwiwa da samun moriyar tare" na kasar Sin.

Haka kuma aikin yana da babbar ma'ana, wajen kara karfafa cudanya da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake kan tsibiran tekun Pasifik a fannonin kiwon lafiya da musayar al'adu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China