in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Beijing a shirye yake ya karbi bakuncin taron kolin FOCAC
2018-08-23 15:29:24 cri





Za a kira taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2018, a tsakanin ranekun 3 zuwa 4 ga watan Satumba mai zuwa a nan birnin Beijing, inda shugabannin kasashen Sin da na Afirka, za su gana da juna domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu. Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, taron kolin da za a gudanar, taro ne mafi kasaita da kasar Sin za ta karbi bakuncinsa, wanda zai samu halartar shugabannin kasashen ketare mafiya yawa a shekarar da muke ciki. Ya kara da cewa, birnin Beijing ya shirya karbar bakuncin taron, zai kuma taryi aminai daga kasashen Afirka, wadanda ke goyon bayan al'ummar kasar Sin a ko da yaushe.

Bisa ga ajandar taron, a ranar 3 da safe, za a fara ne da shirya taron shawarwari a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Afirka da ma wakilan sassan biyu da suka fito daga bangarorin masana'antu da kasuwanci, taron da zai kasance wani muhimmin kashi na taron kolin dandalin FOCAC, inda za a samar da dandali na yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin masu masana'antu na sassan biyu. Har wa yau, a ranar 3 da yamma, za a gudanar da bikin bude taron kolin dandalin FOCAC, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Afirka ta kudu, wato kasar da ke shugabantar dandalin FOCAC tare da kasar Sin, Cyril Ramaphosa, da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame da ke shugabantar kungiyar tarayyar Afirka a wannan karo, da kuma babban sakataren MDD da shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka za su gabatar da jawabi bi da bi. Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, "Yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da wani muhimmin rahoto, inda zai yi cikakken bayani kan sabbin manufofin da gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar, da sabbin matakan da za ta dauka, domin kara kyautata huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, musamman ma a fannonin raya sha'anin samar da kayayyaki, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da cinikayya da zuba jari, da horas da ma'aikata, da ci gaban kimiyya da ba da ilmi da al'adu da kiwon lafiya, da kiyaye muhalli, da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dai sauransu. Wadannan sabbin matakai za su kara biyan bukatun kasashen Afirka ta fannin sake fasalin ci gaban tattalin arzikinsu, haka kuma za su ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata, tare kuma da taka muhimiyyar rawa a fannin ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Afirka, bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni."

Sai kuma a ranar 4 ga wata, za a shirya taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Afirka, inda shugabannin za su yi musayar ra'ayoyi a tsakaninsu dangane da yadda za a bunkasa huldar da ke tsakanin sassan biyu da kuma sauran wasu al'amuran duniya da na shiyya shiyya da ke daular hankalinsu. Bayan taron kuma, shugaba Xi Jinping tare da takwaransa na kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da ma shugaban kasar Afirka da za ta karbi shugabancin dandalin FOCAC daga hannun kasar Afirka ta kudu, za su gana da manema labarai, inda za su bayyana nasarorin da aka cimma a wajen taron.

Chen Xiaodong, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana cewa, taken taron kolin shi ne "hadin gwiwar samun moriyar juna, hada kan juna don tabbatar da makomar bai daya ta Sin da Afirka", taken da ya dace da bukatun bunkasar hadin gwiwar da tsakanin Sin da Afirka, ya ce, "A gun taron, za a kara bayani game da ayyukan da kuma burin da aka sanya a gaba domin tabbatar da makomar Sin da kasashen Afirka ta bai daya. Har wa yau, taron zai kara ma'ana mai armashi ga makomar Sin da kasashen Afirka ta bai daya a sabon yanayin da ake ciki, wato za a yi kokarin ganin makomar za ta kara samun tashe mai inganci da kuma shafar karin fannoni da kafa amfanawa al'umma."

Mr.Chen Xiaodong ya kuma yi nuni da cewa, halin da ake ciki yanzu ya kasance wani muhimmin lokaci na gudanar da hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma nasarorin da za a cimma a gun taron za su haifar da muhimmin tasiri ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa da ma hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Afirka da sauran kasashen duniya. Ya ce, "Taron kolin Beijing da za a kira zai kara kunsa wasu sabbin mambobi uku, wato Gambia da Sao Tome and Principe, da kuma Burkina Faso. Taron zai kuma kara gabatar da wasu sabbin matakai na inganta hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, kuma ba ma kawai ta fannonin raya manyan ababen more rayuwa da kiwon lafiya da cinikayya da kuma ayyukan gona ba, har ma da musayar fasahohi ta fannonin gudanar da harkokin mulki da manufofi da kiyaye muhalli da sauransu."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China