in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Saliyo ya gurfana gaban kotu saboda rashawa
2018-08-23 10:34:09 cri
Tsohon mataimakin shugaban kasar Saliyo, Victor Bockarie Foh, da ministan ma'adanai da albarkatun kasa, Alhaji Minkailu Mansaray da sauran wasu mutane 4 a jiya Laraba suka bayyana a gaban kotu a karon farko bisa zargin aikata laifukan dake da nasaba da rashawa a birnin Freetown.

Ana zargin jami'an da yin sama da fadi da kudaden da gwamnati ta ware wajen tafiyar da harkokin aikin Hajji ga maniyyata musulmi a lokacin aikin Hajjin shekarar 2017. Ana zarginsu da laifuka 8 da kuma wawashe dukiyar gwamnati.

Laifukan sa ake tuhumarsu sun hada da shirya makarkashiya don aikata rashawa, da gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba, da yin zamba da dukiyar gwamnati, da dai sauransu.

An gano an tafka rashawa a ayyukan Hajjin na shekarar 2017 ne bayan da maniyyata musulmi suka yi korafin cewar an damfare su, da tsawwala musu biyan wasu makudan kudade da kuma yaudarar da kwamitin kula aikin hajjin da gwamnatin kasar ta kafa yayi musu.

Hukumar yaki da rashawa ta kasar Saliyo (ACC), ta shafe shekara guda tana gudanar da bincike kan lamarin kuma ta tanadi cikakkun hujjoji bisa tuhumar da take yiwa jami'an da aka samu da hannu. Sabon kwamishinan hukumar ACC, Francis Ben Kaifala shi ne ya jagoranci gayyatar tsohon mataimakin shugaban kasar da sauran wadanda ake tuhuma domin su amsa tambayoyi kan zarge zargen da ake yi musu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China