Zhao ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da manema labarun kamfanin dillancin labaru na Xinhua, inda ya ce, wasu kasashen Afirka da dama na fatan cimma burinsu na dogara da kansu wajen tabbatar da samun ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka, kana suna fatan matsakaita da kanana kamfanoni za su taka muhimmiyar rawa a fannin, musamman ma ta fuskar rayawa da amfani da manyan kayayyakin more rayuwa na sadarwa. Kasar Sin ta samu fasahohi da dama wajen amfani da fasahar sadarwa da matsakaici da kanana kamfanoni ke yi, hakan zai amfana wa hadin kai a tsakanin bangarorin Sin da Afirka.
Ban da wannan kuma, Zhao ya ce, hadin kai tsakanin Sin da Afrika ya samu ci gaba a 'yan shekarun da suka gabata. Taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka da za a shirya a birnin Beijing, zai samar da wani dandali mai kyau na karfafa hadin kansu a nan gaba, wanda ko shakka babu zai daukaka hadin kan sassan biyu zuwa wani sabon matsayi. (Bilklisu)