in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin kasar Morroco ya yi wa mutane 160 afuwa
2018-08-22 10:59:33 cri
Sarkin kasar Morroco Mohammed VI, ya yi wa mutane 160 afuwa, wadanda ke da hannun a zanga-zangar da ta haifar da tashin hankali a yankin Rif da ke arewacin kasar a karshen shekarar 2016.

Kafar yada labarai ta yanar gizo ta Le360.ma, ta ruwaito majiyarsu a ma'aikatar shari'a na cewa, afuwar ta zo ne a daidai lokacin da ake murnar bikin babbar sallah.

Wata sanarwar da ma'aikatar shari'a ta kasar ta bayar a wannan rana, ta bayyana cewa, Sarkin ya yi wa mutane 889 afuwa a lokacin bikin, amma ba a bayyana laifukan da suka aikata ba.

Sai dai kuma, afuwar ba ta shafi jagororin masu zanga-zangar ba, wadanda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.

A karshen watan Yuni ne, kotun kasar Morroco ta yanke wa Nasser Zefzafi, jagoran masu zanga-zangar da ma wasu shugabanninsu uku, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kurkuku. A yayin da aka kuma yanke wa wasu 49 daurin shekaru 15 tare da biyan tara.

Hukuncin ya harzuka mutane a fadin kasar, inda aka ta yi gangami don neman a sako masu zanga-zangar da aka hukunta.

Zanga-zangar ta auku ne a watan Oktoban shekarar 2015, bayan da aka murkushe Mouhcine Fikri, mai sayar da kifi har lahira, sakamakon hawa motar daukar kaya da ya yi don dawo da kifinsa da 'yan sanda suka kwace.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China