in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afghanistan ya sanar da shirin tsagaita bude wuta na watanni 3 da kungiyar Taliban
2018-08-20 11:07:41 cri
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya sanar da shirin tsagaita bude wuta da kungiyar Taliban na tsawon watanni 3 bisa sharadin amincewar kungiyar, wanda zai fara aiki daga yau Litinin.

Ashraf Ghani, ya bayyanawa taron bikin ranar 'yancin kan kasar cewa, yayin da bikin babbar Sallah ke karatowa, suna sanar da shirin tsagaita bude wuta da zai fara aiki daga yau Litinin ranar hawan Arfa, zuwa ranar bikin Maulidi, idan har kungiyar Taliban ta amince.

Shugaban ya yi kira ga kusoshin Taliban da su yi maraba da fatan al'ummar kasar na tsagaita wuta na lokaci mai tsawo tare da cimma zaman lafiya.

Ya ce suna kira ga kusoshin Taliban, da su shiryawa hawa teburin sulhu bisa akidu da ka'idojin addinin musulunci, ya na mai cewa gwamnatin kasar ta cire duk wasu abubuwa dake cikas ga batun samun zaman lafiya mai dorewa ta hanyar wadannan matakai da ba ta taba dauka ba.

Sai dai har yanzu, kungiyar Taliban wadda ta yi ta kin amsa bukatar hawa teburin sulhu ta gwamnatin Afghanistan, ba ta mayar da martani game da kudurin Shugaba Ghani na tsagaita bude wuta ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China