in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar Adawa ta kasar Afrika ta Kudu ta lashi takobin yaki da yunkurin mayar da ikon babban bankin kasar karkashin gwamnati
2018-08-20 10:53:30 cri
Babbar Jam'iyyar adawa a Afrika ta kudu wato Democratic Alliance DA, ta lashi takobin yaki da duk wani yunkuri na karbe ikon babban bankin kasar, wanda ta ce dole ne a kiyaye 'yancinsa na cin gashin kai.

Jam'iyyar ta ce babu wata manufa mai ma'ana ga al'umma cikin yunkurin mayar da bankin karkashin ikon gwamnati, sai dai kawai wani muradi na siyasa.

Wannan na zuwa ne bayan wata jam'iyyar adawa ta daban, wato Economic Freedom Fighters EFF, ta mika shirin yi wa babban bankin garambawul ga majalisar dokokin kasar a farkon makon da ya gabata, tana mai neman a cire jarin bangarori masu zaman kansu tare da mayar da jarin bankin ya zama na gwamnati kadai.

Sanarwar da jam'iyyar DA ta fitar a jiya, ta ce mayar da jarin bankin na gwamnati kadai, wani dadadden muradi ne da Jam'iyyar EFF ke da shi siyasance, domin ta samu yin tasiri kan harkokin bankin da ma tsarin bankunan kasar baki daya.

Sake fasalin bankin ya zama batun da aka fi mayar da hankali kan sa, yayin da Afrika ta kudu ke tunkarar babban zabe a 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China