Gwamnatin Genoa ta fitar da wata sanarwar dake cewa, baya ga 'yan asalin Italiya, sauran mutanen da suka rasa rayukansu sun hada da mutanen kasashen Albaniya, da Columbiya, da Chile, da Faransa, da Jamaica, da Romaniya da kuma Peru.
Tuni a ranar 15 ga wata, gwamnatin kasar ta Italiya ta sanar da kafa dokar-ta-baci na tsawon wata 12 a babban yankin Liguria, inda Genoa take, don gudanar da ayyukan ceto gami da na sake gina yankin.
A ranar 14 kuma, wata gadar mota mai suna Morandi Bridge dake Genoa ta rushe, a lokacin da motoci kimanin 30 ke tafiya a kanta. An fara gudanar da ayyukan ceto bayan aukuwar hadarin, zuwa yanzu akwai mutane 8 da suke jinya a asibiti.(Murtala Zhang)