in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka ta dakatar da kudaden raya Syria da take bayarwa
2018-08-19 16:16:19 cri

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya ce, kasarsa ta dakatar da ba da makuden kudaden da take bayarwa da sunan raya kasar Syria.

Shugaba Trump wanda ya sanar da daukar wannan mataki cikin wani sako ta shafinsa na Tweeter, ya ce Amurka ba za ta ci gaba da biyan kusan dala miliyan 230 a kowace shekara da sunan raya kasar ta Syria ba, maimakon haka ya bukaci kasashe masu arziki da su ci gaba da biyan kudaden

Ya ce, maimakon biyan wadannan kudade don gina kasar Syria, zai yi amfani da kudaden wajen gina Amurka da sojojinta da ma kasashen dake tare da Amurkar.

Trump ya ce, a maimakon Amurka kamata ya yi kasar Saudiya da sauran kasashe masu arzikin man fetur dake yankin Gabas ta Tsakiya su fara biyan wadannan kudade.

A ranar Jumma'a da safe ne, aka umarci ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka da ta canja akalar kudaden da ake warewa da nufin raya kasar ta Syria, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa, za ta canje daga kasar.

A ranar 13 ga watan Fabrairun wannan shekara ce, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya sanar da cewa, Amurka ta yi alkawarin samar da dala miliyan 200 don taimakawa yakin da ake yi da mayakan IS da ma ayyukan farfado da kasar Syria.

Sai dai kuma shugaba Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da biyan wadannan kudade a watan Maris, inda ya bukaci a yi masa karin bayani kan yadda ake kashe wadannan kudade, ya kuma bukaci sauran kasashe da su ma su shigo cikin shirin tare da bayar da karin kudade.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China