in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta ce kawo yanzu ba'a samu bullar wata annoba ba tsakanin mahajjata
2018-08-18 16:47:20 cri
Gidan talabijin na Akhbariya ta kasar Saudiyya, ya ruwaito a jiya, ma'aikatar lafiya ta kasar na tabbatar da cewa, kawo yanzu, ba'a samu bullar cututtuka ko annoba ba tsakanin mahajjata.

An dauki kwararan matakan tsaro da na kiwon lafiya don tabbatar da zaman lafiyar mahajjata yayin aikin hajin da za a yi a makon gobe.

Ma'aikatar kiwon lafiyar ta Saudiyya, ta tabbatar da cewa, yanayin kiwon lafiya da kasar take ciki na da kyau. Kuma tuni ta jaddada cewa za ta kara maida hankali kan lafiyar mahajjata, da karfafa hadin-gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO da sauran wasu hukumomin kiwon lafiya na duniya, domin sa ido da bincike kan yanayin kiwon lafiya da ake ciki da kuma sauye-sauyensa a fadin duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China