in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagororin JKS sun saurari rahoto game da allurar rigakafi maras inganci
2018-08-17 10:20:58 cri

A jiya Alhamis ne, zaunanne kwamitin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, ya saurari rahoton bincike game da sarrafa alluran rigakafin haukan kare marasa inganci, da ake zargin kamfanin harhada magunguna na Changchun Changsheng Life Sciences dake nan kasar Sin da aikatawa.

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, wanda ya dora muhimmancin gaske game da wannan batu, ya sha bayyana dacewar tabbatar da hukunci mai tsanani bisa doka, kan dukkanin wadanda ke da hannu cikin aikata wannan ta'asa, da zarar an kammala bincike.

Sakamakon zaman da aka yi na nuna cewa, jim kadan bayan bullar wannan zargi, shugaba Xi ya ba da umarnin kara azama wajen tabbatar da an bankado duk wasu bayanai masu nasaba da matakan kare lafiya, da samar da daidaito ga zamantakewar al'umma.

Karkashin jagorancin kwamitin koli na JKS, hukumar zartaswar kasar ta zauna sau da dama domin gudanar da bincike, baya ga tura tawagar masu nazarin wannan al'amari, domin tantance hakikanin abun da ya wakana.

Kawo yanzu dai kusan dukkanin wadanda aka dorawa alhakin gudanar da bincike sun kammala ayyukan su. Kana sakamakon da aka samu ya nuna cewa, alluran da kamfanin ke samarwa, suna da tasiri ga lafiyar al'umma da kuma tsaron kasa. A hannu guda kuma, an gano cewa kamfanin ya fitar da alluran rigakafi da suka sabawa ka'idoji, da dokokin kiwon lafiya, da nufin samun karin riba, tare da wallafa takardun shaidar masu binciken ingancin magunguna na bogi.

Kaza lika binciken ya nuna cewa, wasu jami'an karamar hukuma, da masu aikin sa ido sun yi sakaci da ayyukan su, wanda hakan ya haifar da manyan matsaloli, ciki hadda rashin cikakkiyar kulawa, da gibi a ingancin alluran da kamfanin ke samarwa, da rashin kyakkyawan tasiri daga alluran da aka yi amfani da su. Don haka zaman da aka yi ya bayyana aniyar shugabancin kasar Sin, na daukar matakan magance matsalar da aka ci karo da ita.

Da suke gabatar da ra'ayoyin su game da abun da ya wakana, mahalarta taron jami'an sun jaddada muhimmancin karfafa dokoki da ka'idoji, da fitar da tsari da manufofi, da aiwatar da hanyoyin sanya ido, da tabbatar da cewa kamfanoni na sauke nauyin dake wuyan su yadda ya kamata.

Kaza lika sun bayyana muhimmancin zakulo karin hanyoyin tabbatar da nagarta da tsare ingancin hajoji, da dakile illar da ka iya bulla daga rashin ingancin su.

Ga alluran rigakafi masu bukatar matukar kulawa da kwarewa wajen sarrafawa, jami'an da suka yi zaman sun amince da cewa, ya zama wajibi a fayyace hukumomi, da masu aikin sa ido mafiya dacewa da lura da aikin samar da su. Kana a samar da kwararrun masu lura da wannan muhimmin sashe.

A wani bangaren kuma, jami'an sun bayyana cewa, ya zama wajibi duk wani kamfani da ya karya doka ya biya diyya mai tsanani, ba kuma za a daga kafa ga kowa ba. Har ila yau mutanen da ke da hannu a aikin samar da alluran rigakafi da ka iya illata lafiyar al'umma, za su fuskanci hukunci mai tsanani, ciki hadda yiwuwar hana su aiki a irin wannan fanni har abada.

Taron ya kuma jaddada aniyar JKS da gwamnatin kasar Sin, da hukumomi a dukkanin matakai, game bukatar koyon darasi daga abun da ya faru, domin tabbatar da ingancin alluran rigakafi a nan gaba.

Sauran matakan da ake fatan dauka a nan gaba kuwa, sun hada da sake gudanar da sabbin alluran rigakafi ga al'umma, kuma bisa tsari madaidaici, da biyan diyya, da samar da yanayin kara inganta gudanar da alluran a nan gaba.

Kwamitin da ya gudanar da zaman, ya kuma bukaci a sauke mataimakin gwamnan lardin Jilin Jin Yuhui daga mukamin sa, kasancewar sa wanda aka dorawa alhakin lura da sashen sa ido na ayyukan samar da abinci da magunguna na lardin, tun daga watan Afrilun shekarar 2017. An kuma bukaci mataimakin shugaban kwamitin bada shawara kan harkokin siyasa na lardin Jilin, Li Jinxiu ya yi murabus daga mukamin sa. Li shi ne mataimakin gwamnan lardin mai lura da sashen samar da abinci da magunguna tsakanin watan Disambar shekarar 2015 da watan Afrilun shekarar 2017.

Sauran wadanda aka bukata su ajiye aiki sun hada da Liu Changlong, da Bi Jingquan. Kana an bukaci wasu karin jami'an da suka hada da Jiang Zhiying, da Jiao Hong, su yiwa kan su fada. Baya ga su akwai kuma wasu karin jami'an kanana 34 da za a tuhuma bisa wannan badakala ta sarrafa alluran rigakafin haukan kare da ta dabaibaye kamfanin Changchun Changsheng Life Sciences na nan kasar Sin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China