in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da maniyata miliyan 1.6 ne suka isa Makka don aikin hajjin bana
2018-08-16 21:08:20 cri
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar a yau Alhamis cewa, sama da maniyata miliyan 1.6 daga sassa daban-daban na duniya ne suka isa kasar domin halartar aikin hajjin bana.

Babban darektan kula da harkokin fasfo na kasar Saudiyya Sulaiman Al Yahya, shi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da kafar talabijin ta Khbariya ta watsa.

A halin da ake ciki, sama da maniyata 233,000 daga cikin kasar ne suka isa birnin Makka, kuma ana saran isowar wasu.

Yahya ya kuma gargadi maniyata dake kokarin shigowa ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa, yanzu haka an hukunta wasu mutane 18 saboda shigo da wasu maniyata da ba su da takardar iznin yin aikin hajji.

Kasar Saudiya dai ta dauki kwararan matakai don hana maniyatan da ba su da takardun iznin yin aikin hajji shiga kasar, don kaucewa aukuwar hadurra sakamakon cunkoson jama'a a wasu sassa na birnin Makka, musamman wuraren Ibadu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China