in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban E 8: Kaso 90 cikin 100 na masu fama da malaria na kasashen Afirka dake kudu da hamadar sahara
2018-08-16 20:30:52 cri
Tsohon ministan lafiya da ayyukan jin dadin jama'a na kasar Namibia Richard Kamwi ya ce, kusan kaso 90 cikin 100 na masu fama da zazzabin cutar cizon sauro a duniya ana samun su ne a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara.

Kamwi ya bayyana hakan ne a gefen taron kolin kasashen kudancin Afirka (SADC) karo na 38 game da kawar da cutar malariya ko E 8 a takaice.

An kafa shirin na E 8 ne tsakanin kasashen kungiyar ta SADC guda 8 wanda Kamwi ke shugabanta, ta yadda za su tsara su kuma aiwatar da matakan kawar da zazzabin na malaria a shiyyar, bayan da aka gano cewa, cutar tana lakume rayukan mutane da dama a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar sahara fiye da sauran cututtuka.

Wani sakamakon bincike game da makomar cutar a nahiyar na shekarar 2018, ya nuna cewa, cutar na yiwa tattalin arzikin nahiyar illar da ta kai sama da dala biliyan 12 a kowace shekara, kana tana rage saurin bunkasar tattalin arzikin kasashen dake fama da cutar ta malaria matuka da kusan kaso 1.3 cikin 100.

Kamwi ya ce idan har aka yi nasarar kawar da cutar, hakan zai taimaka wajen rage matsalar talauci da karfafa ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Kasashen na E 8 sun kunshi Angola, da Bostswana, da Masayeantar Eswatini wato Swaziland, da Mozambique da Namibia da Afirka ta kudu da Zambia da kuma Zimbabwe.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China