in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OCHA ta bukaci a ba fararen hula kariya a yankuna masu fama da rikici
2018-08-16 10:24:32 cri

Ofishin dake kula da hakkin dan adam na MDD (OCHA) ya gabatar da koke ga shugabannin duniya, inda ya nemi a ba da kariya ga fararen hula da jami'an kai agaji a yankunan da ake fama da tashe tashen hankula.

Hukumar ta gabatar da koken nata ne a yayin da ake shirin gudanar da bikin ranar kare hakkin dan adam ta duniya, wanda ta fado a ranar 19 ga watan Augasta.

A sakon da OCHA ta gabatar, ta ce, a ko wace shekara ana gudanar da bikin ranar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ne domin nuna goyon baya ga miliyoyin mutanen da rikice rikice suka shafa da ma'aikatan bayar da agaji da kuma jami'an kiwon lafiya wadanda suke jefa rayuwarsu cikin garari domin taimakawa al'ummar dake fuskantar tashin hankali. Hukamar ta ce, ana amfani da wannan rana ce domin tunawa duniya irin nauyin dake wuyan kowa wajen fafutukar tsame mutane daga cikin tashin hankali.

Hukumar ta ce, a halin da ake ciki a wannan lokaci, a wuraren da ake fama da tashe tashen hankula, ana yawan hallaka fararen hula, da raunata su, ana kuma lalata garuruwa da birane a hare haren da ake yawan kaddamarwa. Ana raba mutane da hanyoyin samun abinci, da ruwan sha da hana su samun tallafi, a wasu lokutan ma ana jefa su cikin matsalar yunwa da gangan a matsayin wani salon a dabarun yaki.

Sakon ya kara da cewa, an karkashe jami'an ba da agaji da ma'aikatan kiwon lafiya, a raunata su, ko kuma yin garkuwa da mutane ko hana su damar kaiwa ga mutanen dake bukatar dauki.

An gudanar wannan kira ne yayin da ya rage wata guda za'a gudanar da babban taron shugabannin duniya a New York, inda za'a gudanar da babban taron mahawara na MDD da aka saba gudanarwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China